in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna rashin gamsuwa game da sakamakon kuri'ar raba gardamar Crimea
2014-03-18 14:23:27 cri
Jiya Litinin 17 ga wata, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa, inda ya nuna rashin jin dadinsa dangane da sakamakon kuri'ar raba gardamar da al'ummar yankin Crimea suka kada, a sa'i daya kuma, ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kaucewa daukar matakan da ba su dace ba.

Sanarwar ta kuma nuna cewa, har kullum Mr. Ban na kira ga bangarorin da rikicin kasar Ukraine ya shafa, da su kaucewa daukar matakan da suka sabawa doka, a wannan lokaci da ake fuskantar rashin fahimtar juna a yankin.

Ban da haka, ya kuma sa kaimi ga bangarorin da wannan batu ya shafa, da su lalubo hanyar warware rikicin bisa ka'idojin MDD, tare da nuna girmamawa ga ikon mulkin kasar Ukraine da dinkuwar kasar.

Daga nan sai Ban K-moon ya yi Allah wadai da zub da jinin da ya auku a gabashin kasar Ukraine a kwanan baya, ya na mai kira ga bangarorin masu ruwa da tsaki, da su shiga shawarwarin wanzar da zaman lafiya tsakaninsu, tare da kaucewa rikice-rikcie a duk fadin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China