Firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ta bayyana cewa, kowane irin takunkumi ba zai iya korar mutanen da suke son gudanar da kasuwanci a kasar ta Rasha ba. Ban da haka, wani masanin kasar ya ce, babu takunkumin da zai iya lalata tsarin masana'antun tsaron kasar da kuma matsayin kasar a kasuwar makamai ta duniya.
A ranar 25 ga wata, karo na farko ne hukumar Crimea ta fara biyan kudin fensho da kudin Rasha na Ruble ta gidajen wayan yankin. A wannan rana kuma, majalisar dokokin kasar Ukraine ta nada janar Mykhailo Koval a matsayin sabon mukaddashin ministan tsaron kasar, wanda bayan nadin ya bayyana cewa, Ukraine za ta janye dukkanin sojojinta daga Crimea.
Har wa yau, babban sakataren MDD ya bukaci Rasha da Ukraine da su tuntubi juna kai tsaye, a yayin da shi ma yake kokarinsa a wannan fanni.(Lubabatu)