in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara amfani da kudin Rasha a Crimea
2014-03-24 16:10:13 cri

Bisa labarin da kafar dillancin labaru ta "Interfax" mallakar kasar Ukraine ta yada, an ce tun daga yau Litinin din nan, an fara yin amfani da kudin Rasha wato Ruble a yankin Crimea.

Wani jami'in gwamnatin Crimea ya bayyana cewa, tun daga ranar ta 24 ga wata, za a iya amfani da ko dai kudin Ukraine na Hryvnia, ko kuma kudin Rasha na Ruble.

Shugaban Bankin Crimea ya sanar a ran 23 ga wata cewa, za a yi amfani da Hryvnia da Ruble a lokaci daya, har zuwa ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2016, inda Ruble zai zama kudin da ya fi muhimmanci wajen amfani a Crimea. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China