in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Nijeriya ya samu bunkasa a fannoni daban-daban
2014-04-11 10:56:44 cri

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a yanzu haka, jimilar GDPn tarayyar Nijeriya ta kai dala biliyan 510, wanda hakan ya sanya kasar kasancewa a matsayi na 26 a duniya, kuma a matsayi na farko a nahiyar Afirka a fannin karfin tattalin arziki. Wannan dai mataki ya nuna cewa, Nijeriyar ta samu bunkasuwa a fannoni daban-daban.

Kafofin yada labaru na kasar sun bayyana cewa, karuwar jimilar GDP a ko wace shekara daga shekarar 2010 zuwa ta 2013, ya kai kaso 6.39 bisa dari. Inda sha'anin ba da hidima ya fi samun bunkasuwa da kashi 7.7 bisa dari a ko wace shekara, sai sha'anin kere-kere dake biye wanda ke karuwa da kaso 7 bisa dari a ko wace shekara.

Hakan dai ya sanya Nijeriya tunkarar matsayi na 20 a duniya, a fannin tattalin arziki kafin shekarar 2020.

Ban da haka kuma, bisa kididdigar da aka fitar, an bayyana cewa, sha'anoni mafiya girma a kasar su ne noma, da cinikayya, da sashen man fetur, da sadarwa da kuma gidaje. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China