Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kame wadansu mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne a jihohin Adamawa da Taraba dake arewa maso gabashin Nigeriya,a yayin da suke kokarin arcewa zuwa kasar kamaru.
Wata sanarwa da Darekton Tsaro na yada labarai Chris Olukolade, ya aika zuwa ga kamfanin dillacin labarai na Xinhua, ta bayyana cewar 'yan ta'addan an rutsa da su ne a cikin wani shiri da rundunar sojin na Nijeriya ta kaddamar da zimmar kara kaimin sintiri a iyakokin Najeriya da Kamaru da Chadi
Sanarwar ta ce a bisa dukkan alamu, wasu daga cikin 'yan ta'addan sun kasa hakurin fama da yunwa a sansanonin su dake cikin daji.
Darekton Tsaro na yada labarai Chris Olukolade, ya ce wadanda aka cafke sun yi wa sojojin Nigeriya jagora ya zuwa maboyar yan ta'addan, a inda hakan yasa aka gwabza kazamin fada, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ta'adda bakwai, sannan kuma aka sami nasarar kwace na'urori na bam da bindigogi da kuma mashuna saba'in.
Kamar dai yadda Kakakin rundunar sojin ta Nijeriya, ya bayyana wata arangamar ta dabam da aka yi a garin Gumbi, ta haddasa hallaka 'yan ta'adda hudu.
Olukolade ya ce kara kaimin farmaki a maboyar 'yan ta'adda, a kan iyakoki, tayi sanadiyyar cafke wasu yan taadda, ciki har da wani sojin haya dan kasar Chadi da Burkina Faso, wanda kuma ke dauke da muggan makamai.
Kakakin rundunar sojin ta Nijeriya, ya bayyana cewa a yanzu rundunar na kara kai farmaki a maboyar 'yan ta'adda a wadannan iyakoki na kewayen tafkin Chadi da suka hada da Kwatan, Kanwa, Kwatan Yobe da sauran wadan su tsibirai dake yankin. (Suwaiba)