in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya sauke ministan wasanni ya kuma nada wassu sabbin ministoci 11
2014-03-05 20:42:30 cri
Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya a laraban nan 5 ga wata ya sanar da sauke ministan wassanni da motsa jiki Bolaji Abdullahi daga mukamin sa a ci gaba da yake na gyaran fuska a gwamnatin shi.

A wani bangaren kuma ya nada sabbin ministoci 11 a safiyar yau din wanda a ciki ya nada Tamuno Dagogo ya maye gurbin Bolaji Abdullahin na ma'aikatar wassanni da motsa jiki da yake kan mukamin tun shekara ta 2011 wanda kuma aka sauke a yanzu.

Wannan sanarwar tazo ne jim kadan kafin a fara zaman majalissar zartaswa da a kan yi duk mako a fadar Shugaban kasar dake Abuja babban birnin tarayyar kasar dake yammacin Afrika.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China