Kakakin hukumar ya bayyana wa manema labarai cewa, hadarin ya faru ne a wani tabki dake karamar hukumar Festac, inda masu aiki ceto suka ceci mutane 5, amma ya zuwa yanzu, mutane 6 sun bace.
Kakakin ya kara da cewa, dukkan mutanen dake cikin jirgin ruwan mazauna wurin ne, kuma mai iyuwa ne, daukar mutanen da ya fi karfin jirgin shi ne ya haddasa kifewarsa. (Maryam)