140323murtala.m4a
|
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna, dake arewacin Najeriya ta bayyana cewa, yawan masu kauracewa gidajen su, daga kauyuka ukun da aka kaiwa farmaki kwanan baya a jihar na ci gaba da karuwa.
Babban sakataren hukumar ta SEMA, Mista Dogo Makama ne ya bayyana haka a Kaduna, yana mai cewa a halin yanzu, hukumar tayi rajistar 'yan gudun hijira 2000, daga karamar hukumar ta Kaura, tare da bayyana tabbacin basu kulawar da ta dace.
Makama ya kara da cewa, sakamakon wani binciken farko da suka gudanar a kauyukan da abin ya shafa, sun gano kimanin gidaje 240 ne aka kone yayin hare-haren, yayin da kuma aka kashe mutane 119, baya ga wasu mutane 22 da ke ci gaba da karbar magani sakamkon raunukan da suka samu.
A cewarsa, an tsugunar da 'yan gudun hijirar ne a makarantar sakandaren Bandon, inda aka fara raba masu kayayyakin masarufi da na abinci.
Sakataren hukumar ta SEMA ya kuma jajantawa al'ummomin da al'amarin ya shafa, ya na mai alkawarta cewa, nan ba da jimawa ba za a mayar da su gidajensu na asali.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.