in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta jagoranci bunkasuwar yammacin Afirka, in ji Bankin raya Afirka
2014-03-27 10:35:41 cri

Rahoton da Bankin raya Afirka ya gabatar a 'yan kwanakin baya ya nuna cewa, Nijeriya ta jagoranci bunkasuwar tattalin arziki a yammacin Afirka.

Rahoton ya ce, a yankin Afirka da ke kudu da Sahara, yawan kamfanonin da darajarsu ta wuce dala biliyan ya kai 12, 11 daga cikinsu kamfanonin Nijeriya ne. A cikin manyan kamfanoni 50 na yammacin Afirka, kamfanoni 44 sun zo daga Nijeriya.

A sa'i daya kuma, rahoton ya ce, yammacin Afirka na fuskantar wasu matsaloli wajen samun bunkasuwa, yawancin kamfanoni kanana ne, yawancin manyan kamfanoni suna cikin Nijeriya, wadanda suka shafi bankuna, da sadarwa, da masana'antu kuwa, yanayin kasuwanci a yammacin Afirka ba shi da kyau, wanda yake bukatar kyautatuwa, mugun yanayin kasuwanci a yammacin Afirka ya kan janyo a sassan kudade da yawa ga 'yan kasuwa da suke gudanar da ayyukansu.

Rahoton ya ci gaba da cewa, a gaban wadannan matsaloli, idan ana son sa kaimi ga raya wannan yanki bai daya, to, goyon baya da Nijeriya ke nunawa yana da muhimmancin matuka. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China