Bisa labarin da wata kafar watsa labaru ta Nijeriya ta bayar a 'yan kwanakin baya, an ce, bayan da gwamnatin kasar ta yi la'akari sosai da tasirin da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci zai haifar a kasar, Nijeriya ta ki yarda da daddale yarjejeniyar da kungiyar tarayyar Turai ta gabatar a karkashin yarjejeniyoyin bangarori biyu musammun ma ta fuskar tattalin arziki tsakanin EU da gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS.
Bisa shirin yarjejeniyar tsakanin EU da ECOWAS, an ce, nan take ne kungiyar EU za ta bude kasuwar cikakkiya ga kasashe 15 na ECOWAS da Mauritania. A nata bangare, sannu da hankali ne, ECOWAS za ta bude wa EU kasuwanninta da kashi 75 bisa dari, mai yawan al'umma miliyan 300, bisa wa'adin tsawon shekaru 20. Ban da wannan kuma, a cikin shekaru 5 masu zuwa, EU za ta bayar da taimakon kudi Euro biliyan 6.5 ga kungiyar ECOWAS, domin rage babbar illa da take fuskata sakamakon shiga cikin bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya.
Kafar ta ambato maganar ministan ciniki da masana'antu da zuba jari na Najeriya mista Aganga cewa, idan an daddale yarjejeniyoyin tsakanin EU da ECOWAS, to, ba za a iya samun taimako ga bunkasuwar tattalin arziki a Nijeriya cikin dogon lokaci ba. Ministan ya ce, idan Nijeriya ta yi watsi da bunkasuwar masana'antu, don kara bude kofa wajen shigar da kayayyaki daga kasashen waje, gwamnatin Nijeriya za ta asarar kudaden shiga masu yawan gaske, haka kuma, wannan zai janyo babbar illa ga samar da guraban ayyukan yi ga jama da zuba jari. (Danladi)