in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matasa sun kone majami'u biyu a jihar Katsina sakamakon kalaman batanci ga Musulunci
2014-04-01 16:42:13 cri






Wasu matasa sun kone wasu majami'u guda biyu, a yankin Tudun Wada na karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina a tarayyar Najeriya, sakamakon kalaman batanci ga addinin Musulunci da ake zargin wani malamin makaranta ya yi, kamar yadda wadanda abin ya faru a gaban idonsu suka bayyana.

Hargitsin na yammacin litinin ya faru ne bayan da wasu daliban makarantar sakandare mai zaman kanta, mai suna Ideal School, suka yi korafin cewa wani malami mai hidimar kasa, wanda a cikin tambayoyin da ya shirya musu na jarrabawa ya hada da wasu da suke nuna batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Bayan wannan korafi ne kuma wasu gungun matasan yankin suka fusata, suka nufi makarantar da zummar kone ta kurmus, sai dai a cewar wani Alhaji Surajo, ba su sami nasarar hakan ba, saboda kafin su karasa, jami'an tsaro sun isa makarantar.

Ganin haka ne matasan suka shiga lalata kayayyaki, kafin daga karshe su kone majami'un biyu.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China