in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga rana ta 7 da bacewar jirgin saman kasar Malasiya
2014-03-14 11:24:46 cri

A yau an shiga rana ta 7 da bacewar jirgin saman fasinjan nan na kasar Malasiya, wanda ke dauke da matafiya 239, ciki hadda 'yan kasar Sin 154. Duk kuma da dukufar da masu ruwa da tsaki suka yi domin gano inda wannan jirgi ya shiga hakansu bai cimma ruwa ba.

Kasashen da yankuna kimanin 10 da suka hada da Malasiya, da Vienam, da Sin, da Amurka na ci gaba da ba da gudummawarsu ga aikin laluben jirgin.

Bugu da kari cibiyar aikin ceto a teku ta kasar Sin ta bayyana cewa, ya zuwa karfe 12 na tsakar ranar 13 ga watan nan, rukunonin masu ceto kasar sun kwashe sa'o'i 100 ko fiye suna aikin lalube a fadin yankuna da suka kai muraba'in kilomita 45,763, sai dai har ya zuwa wannan lokaci ba a samu wani sakamako mai alaka da inda jirgi ya shige ba.

Direktan cibiyar He Jianzhong ya bayyana cewa, cibiyar za ta kira wani taron masana a yau Jumma'a 14 ga wata, inda masana daban-daban, da kuma wakilan hukumar aikin ceto a teku da sassanta za su tattauna kan halin da ake ciki don gane da wannan aiki, da ma fidda tsarin shiri na gaba.

A wani ci gaban kuma, kakakin fadar Amurka Jay Carney ya bayyana ra'ayinsa kan wannnan lamari, yana mai cewa bisa rahotannin baya bayan nan masu alaka da shirin bincike, kila za a binciki wani yanki na tekun Indiya, kwamitin kula da tsaron zirga-zirgar kasar, da kuma hukuma mai kula da zirga-zirga a sararin samaniya suna bincike kan dalilin bacewar wannan jirgi, kuma Amurka a cewarsa na iyakacin kokarinta wajen gano dalili rashin samun wata shaida mai inganci kan abin da ya faru ga jirgin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China