Mukadashin ministan kula da harkokin sufuri na Malaysia Hishamuddin Hussein ya bayyana a wani taron manema labaru da aka yi a safiyar wannan rana cewa, watakila jirgin saman fasinjan da har zuwa yanzu ba a san inda yake ba ya juya, kafin a daina ganinsa a na'urar sakamakon tilasta masa da aka yi. Don haka za a fadada binciken da ake yi, a kokarin tabbatar da wurin da jirgin saman yake cikin hanzari.
Har wa yau, sufeton hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta Malaysia ya bayyana a wannan rana a taron manema labaru da aka saba shiryawa a filin jirgin sama na kasa da kasa da ke birnin Kuala Lumpur cewa, an tabbatar da cewa, fasinjoji 2 da ke cikin wannan jirgi sun yi amfani da fasfon boge, amma bai fayyace kasashen da fasinjojin 2 suka fito ba. (Tasallah)