A yadda gidan rediyon yace,ya yada rahoton ne bisa sanarwar da ta fito daga ofishin shugaban kasar da na majalissar Ministoci.
Rahoton gidan rediyon yace ba wani dalili da aka bayar na wannan mataki kuma a al'adance Shugaban kasa nada hurumin kin bada dalilai.
Magatakardar ayyukan kasar,Chinthu Phiri a yadda radiyon Zodiak online wata gidan rediyo a Malawi, ya jiyo a cewar shi Shugaban Kasar ya dau wannan mataki bisa ga damar da kundin tsarin mulki ya ba shi.
Amma kuma,rusa majalissar Ministoci ya zo ne a wani muhimmin lokaci da Malawin ke ja'in ja da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma yan adawan jam'iyun siyasa game da yadda Gwamnatin Mutharika ya tafiyar da mulkin sa,in ji gidan rediyon.
Kungoyoyi masu zaman kansu sun kalubalanci Shugaba Mutharika lokaci zanga zangar lumana ran 20 ga watan jiya tare da yin watsi da kiran addu'o'i na musamman a duk fadin kasar ranar 17 ga wannan watan agusta don samar da damar shawarwari da juna.