A ran 10 ga wata da dare, Mahukuntan birnin Beijing, da ma'aikatar harkokin wajen Sin, da ma'aikatar zirga-zirga ta Sin, da hukumar kula da jiragen sama ta jama'a ta kasar Sin sun shirya taron manema labaru tare, inda suka bayyana halin da ake ciki game da kasa tumtubar jirgin sama na Malaysia.
A gun taron, mataimakin darektan cibiyar ceto a kan teku, kuma babban Jami'I a ofishin kula da harkokin yau da kullum na ma'aikatar zirga-zirgar Sin Mista Zhuo Li ya bayyana cewa, bayan da jirgin ruwa mai lamba '115 na kudancin teku' ya isa wurin a ran 10 ga wata da dare, ya hadu da sauran jiragen ruwa da suka shiga aikin ceto a tekun suka zama 3, ana sa ran a daren talatan nan 11 ga wata, karfin ceto na kasar Sin zai kai jiragen ruwa 6 tare da jiragen sama masu saukar ungulu 3.
Mataimakin darektan ofishin jakadancin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mista Zhai Leiming shima ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya tattauna sau biyu da iyalan mutanen da suke cikin jirgin tare da sauraran damuwar su. Ya kara da cewa, ma'aikatan hukumar kula da jakadanci na ma'aikatar harkokin wajen Sin da ofisoshin jakadancin Sin da ke kasashen waje sun gana da bangarorin daban daban dangane da hakan a kokarin samun wani cigaba akan hakan kafin su dawo gida.
A wannan ranan kuma, babban sakataren zartaswa na kwamitin share fage na hukumar kula da yarjejeniyar haramta gwajin nukiliya ta MDD ya bayyana a cibiyar Majalissar cewa, ya
Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya buga waya ga ofishin kula da harkokin jakadancin ma'aikatar harkokin wajen Sin, domin fahimtar sabon ci gaban da aka samu game da neman jirgin saman