in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an Sin da Malaysia sun gana da juna kan batun jirgin nan da ya bace
2014-03-13 11:16:00 cri

Jami'ai daga kasar Sin da takwarorin su na kasar Malesiya, sun gana da juna a nan birnin Beijing, don gane da batan jirgin fasinjan nan na kasar Malasiya.

Jami'an da suka halarci taron na ranar Laraba 12 ga wata, sun hada da mataimakin ministan harkokin wajen Sin Mista Xie Hangsheng, da mataimakin daraktan hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta jama'ar kasar Sin Mista Xia Xinghua, da mataimakin magajin birnin Beijing Mista Zhang Yankun. Sauran jami'an sun hada da manzon musamman mai kula da harkokin Sin na firaministan Malaysiab Huang Jiading, da jakadan Malaysia a Sin Iskandar Sarudin, da wakilan hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta Malaysia, da na kamfanin jiragen saman kasar ta Malaysia.

Yayin taron wakilan Sin sun bayyana cewa, a halin yanzu bangarori daban daban, suna iyakacin kokarin gudanar da aikin ceto, amma ba a kai ga gano jirgin ba tukun. Kuma iyalan fansinjoji, da gwamnatin Sin da jama'arta sun damu matuka game da batan jirgin.

Don gane da hakan ne kasar Sin ta yi kira ga gwamnatin Malaysia, da kamfanin jiragen saman ta, su bayar da hakikanin bayanan da suka tattara a kan lokaci, su kuma gabatar da matsayin aikin da suke yi, tare da amsa tambayoyin da iyalan fansinjojin ke bukatar gabatarwa, da kwantar da hankulansu, kasancewar Sin na da burin ba da taimakon ta cikin yakini.

A nasu bangare, wakilan kasar Malaysia sun bayyana cewa, kasar tana nauyin daukar matakan shawo kan wannan matsala yadda ya kamata. Inda a yanzu haka take ci gaba da ganawa da bangarori daban daban kan wannan batu, baya ga ingatan aikin ceto da take yi. Domin biyan bukatar iyalai da kasar Sin, bangaren Malaysia zai shirya taron watsa labaru, don sanar da ci gaba da aka samu, tare da yin iyakacin kokari wajen biyan bukatar iyalan fasinjojin.

Har wa yau dai a wannan rana ne, yayin taron nazarin ayyukan sana'ar zirga-zirgar jiragen sama na duniya na shekarar bana, sakataren kwamitin hadaddiyar kungiyar zirga-zirgar jiragen sama ta duniya Mista Tang Yanlin ya yi nuni da cewa, tabbatar da tsaron lafiyar jama'a ne babban aiki na farko, dake gaban sashen kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, kuma masana'antun za su kara kyautata kwarewarsu, a fagen kula da harkokin inganta fasahohi, don kare aukuwar hadurra.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China