A cewar kakakin rundunar soja kasar, jirgin da rundunar mayakan kasar ta aika, zai yi kokarin jiyo sautin akwatin da ke nadar bayanan jirgin a saman ruwan da ake zaton nan ne wurin da jirgin ya bace.
Dubban jiragen ruwa daga kasashe daban-daban ne suka shiga aikin gano jirgin, inda ya zuwa ranar Laraba da rana jiragen ruwan kasar Sin guda 8 ciki har da jiragen yaki 3 sun gudanar da bincike a kan ruwa ba tare da gano baraguzai ko wasu sassan jirgin ba, yayin da ake saran isowar karin jiragen ruwa.
A halin da ake ciki kuma, kasar Sin ta samar da karin taurarin dan adam guda 10 wadanda za su kara taimakawa a kimiyance a kokarin da ake yi na gano wannan jirgi samfurin Boeing 777-200, da ake saran zai sauka a Beijing da misalin karfe 6 da minti 30 na safiyar ranar Asabar da ta gabata, amma har yanzu ba a ji duriyarsa ba. (Ibrahim)