Mai rikon mukamin ministan sufurin kasar Malaysia Hishammmuddin Husseine ne ya bayyana hakan a yau yayin wani taron manema labarai. Ya ce aiki na karshe da jirgin ya yi kamar yadda na'ura ta nuna ita ce da karfe 1 da minti 7 na safe agogon wurin kuma a lokacin jirgin ba shi da wata matsala.
Bugu da kari jami'in ya ce, ba a samu komai ba a wuraren da tauraron dan adam na Sin ya nuna wasu abubuwa guda 3 suka yawo a kan ruwa a kokarin da ake na neman jirgin saman kasarta Malaysia kirar MH370 da ya bace tun ranar Asabar din da ta gabata.
Kasashe da dama ne yanzu haka suka agaza da kayayyakin ceto don taimakawa wajen gano jirgin, amma har yanzu babu wani labari game da jirgin.
Yanzu haka akwai jiragen ruwa 43 da jiragen sama 48 da ke aikin gano jirgin, yayin da wasu jiragen ruwa 26 da na sama 25 ke nasu aikin gano jirgin a yankunan kudancin tekun kasar Sin. (Ibrahim)