Jirgin saman mai dauke da fasinjoji 39 da ma'aikatan jirgi 4 ya fadi ne jim kadan da ya tashi daga babban garin Tyumen, kusan kilomita 2,100 daga gabashin Moscow zuwa Surgut wani gari a yankin Siberiyan.
Masu lura da zirga zirgan jiragen sama na filin jirgin sun ce jirgin ya bace daga na'urar dake nuna zirga zirgan jiragen kuma suka kasa samun shi a layin sadarwa jim kadan da tashinsa.
Tun da farko dai rahotanni daga kamfanin dillanci labaru na kasar, Itar-Tass ya ce fasinjoji 39 ne ma'aikatan jirgi 2 a cikin jirgin kuma dukkan su sun mutu.
An gano kwatin adana bayanai guda biyu na jirgin amma har yanzu ba a san dalilin da ya kawo faduwar jirgin ba
Masu bincike na kasar Rasha sun fara bincike game da laifin da ya faru ya zama wannan abin bakin ciki.(Fatimah Jibril)