in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bayar da umarnin gudanar da bincike game da musabbabin faduwar jirgin sama mai saukar ungulun da ya yi sanadiyar mutuwar wasu jami'an kasar
2012-12-16 16:19:07 cri

A ranar Asabar da dare ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya bayar da umarnin gudanar da bincike ba tare da bata lokaci ba, dangane da musabbabin faduwar jirgin mayakan ruwan kasar mai saukar ungulu wadda ya yi sanadiyar mutuwar gwamna Patrick Yakowa na jihar Kaduna da tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Laftana Janar Andrew Owoye Azazi mai ritaya.

Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya samu daga ofishin shugaban wadda ya bayar da umarnin gudanar da binciken, ta ce shugaban ya kadu matuka dangane da hadarin jirgin na ranar Asabar da ya faru a jihar Bayelsa.

A cewar sanarwar, shugaban ya mika ta'aziyyarsa ga iyalai da abokan mamatan da kuma gwamnatoci da al'ummar jihohin Kaduna da Bayelsa.

Ya bayyana mutuwar wadannan jami'an kasar a matsayin babban rashi ga daukacin kasar.

A halin da ake ciki kuma, a ranar Asabar ne, ita ma gwamnatin jihar Kaduna da ke tsakiyar arewacin Najeriya, ta bayar da sanarwar mutuwar gwamnatin jihar Patrick Ibrahim Yakowa, wanda ya mutu sanadiyyar wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Bayelsa.

Wata sanarwa mai dauke da sanya hannun sakataren gwamnatin jihar ta Kaduna Lawal Sama'ila Abdullahi, ta ce gwamnan ya mutu ne a wani hadarin da ya rutsa da shi a wani jirgin mayakan ruwan kasar mai saukar ungulu, a kan hanyarsa ta zuwa garin Fatakwal daga jihar Bayelsa.

Ita ma jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, gwamna Yakowa ya mutu a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Bayelsa. Bugu da kari sanarwar ta bayyana cewa, shi ma tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro janar Andrew Azazi ya mutu a cikin hadarin.

A halin da ake ciki kuma, hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa a Njeriya(NEMA) ta ce, an gano gawawwakin mamatan da hadarin ya rutsa da su a ranar Asabar da rana a jihar Bayelsa da ke kudu maso gabashin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China