Ma'aikatar tsaro da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama da ma kamfanin jirgin duk sun tabbatar da wannan labari.
Jirgin da ke dauke da fasinjoji 118 tare da ma'aikatan jirgin 9 ya tashi a wannan rana da yamma daga birnin Karachi da ke kudancin kasar zuwa Islamabad. Da misalin karfe 6 da minti 50, agogon wurin, jirgin ya fado a wani wurin da ke da tazarar kilomita 10 zuwa 20 da birnin Islamabad a yayin da yake yunkurin sauka a filin jirgi na birnin.
A cewar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Pakistan, ana ruwa kamar da bakin kwarya a lokacin aukuwar hadarin.
A labarin da kafofin yada labarai na wurin suka bayar, an ce, jirgin ya fado a unguwannin jama'a, kuma hadarin ya sa tashin gobara a gine-gine sama da 40, tare da yin sanadiyyar mutuwar mutane a wurin da kuma jimuwarsu.
Bayan aukuwar hadarin, asibitoci a Islamabad da kuma Rawalpindi sun sanar da shiga halin gaggawa. Baya ga haka kuma, ministan tsaro na kasar shi ma ya ba da umurnin bin bahasin hadarin. (Lubabatu)