in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kananan jakadun kasashe 7 da ke birnin Lagos sun nuna juyayi game da hadarin jirgin sama da aka samu a Nijeriya
2012-06-06 20:27:31 cri

A ranar 5 ga wata da yamma, karamin jakadan Sin da ke birnin Lagos Liu Xianfa da sauran kananan jakadun kasashe 6 da ke birnin Lagos sun nuna juyayi ga mutane 'yan Nijeriya da na kasashensu da suka rasu cikin hadarin jirgin sama da ya abku a kasar Nijeriya. Kuma sun yi shawarwari da gwamnatin jihar Lagos, hukumomin ba da umurni a wurin, da hadarin ya faru domin batun hadarin jirgin sama don gano gawawwakin mutanen da suka rasu, da kammala sauran ayyuka.

Kananan jakadun kasashen Amurka, Lebanon, Faransa, Jamus, India, Indonesiya da Sin, sun yi shawarwari tare da bangaren hukumomin jihar Lagos, kuma bisa labarin da aka samu, a cikin mutanen da suka rasu cikin faduwar jirgin sama a ranar 3 ga wata, akwai mutanen kasashen waje 21 a cikin jirgin, wadanda suka hada da Sinawa 6, da Amurkawa 8, da 'yan kasar Lebanon 2, da dan kasar Canada, Faransa, Jamus, India, da Indonesiya.

Mataimakin karamin jakadan Sin da ke Lagos Qiu Jian ya sanar da cewa, bayan da kungiyar aiki ta karamin ofishin jakadancin Sin da ke Lagos da ma'aikatan kamfanin kasar Sin sun yi bincike game da gawawwaki sama da 100, an gano gawar basine guda, ya ce, bisa takardar sunayen da aka samu daga kasar Nijeriya, an ce, yawan Sinawa da suka rasu cikin hadarin jirgin sama da aka samu a ranar 3 ga wata ya kai 6.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China