in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun mika sakwannin ta'aziyya ga takwarorinsu na Pakistan kan hadarin jirgin sama
2012-04-21 21:05:18 cri
Wani jirgin saman fasinja na kasar Pakistan ya fado a ranar 20 ga wata a kusa da Islamabad, babban birnin kasar, hadarin da ya yi sanadiyyar dukannin mutane 127 da ke cikin jirgin.

A ranar 21 ga wata, shugaban kasar Sin ya aika sako ga takwaransa na kasar Pakistan, Asif Ali Zardari, inda a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar da kuma shi kansa, ya nuna tausayi ga wadanda suka mutu a sakamakon hadarin tare da jajanta wa iyalansu.

Ban da haka, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao da ma ministan harkokin waje na kasar, Yang Jiechi su ma sun mika sakwannin taya bakin ciki ga takwarorinsu na kasar ta Pakistan.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China