A ranar 8 ga wata, wani jirgin sama samfurin Boeing 727 mallakar kamfanin Hewa Bora Airways ya yi hadari a yayin da yake kokarin sauka a filin jirgin saman birnin Kisangani. Ya zuwa yanzu, babu wani takamaiman bayani game da yawan mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin. Jami'ai a asibitin birnin Kisangani sun ce, mutane 77 ne suka mutu, amma a cewar masu agaji na kungiyar Red Cross, gawawwaki 74 ne kawai suka gano. A sa'i daya, ma'aikatar sufuri ta kasar ta ce, hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 127, a yayin da wasu 51 suka samu damar tsira da rayukansu.(Lubabatu)