A wannan rana, daliban da makarantun birnin Lagos guda 19 suka zaba sun halarci gasar, kuma wakilai sama da dari 5 daga bangaren da ya shafi al'adu, sha'anin kasuwanci na kasar Nijeriya, karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Lagos, kungiyar 'yan kasuwa da kamfanoni na kasar Sin dake kasar Nijeriya sun kalli gasar da aka yi a jami'ar.
Bayan wannan gasa, mahalartar gasar sun nuna kaunarsu game da kasar Sin da kuma al'adunta, tare da nuna godiya ga kwalejin Confucius da ya shirya gasar, ta hanyar nuna abubuwan da suka koyo dangane da kasar Sin.
Shugabar kwalejin koyon Sinanci na Confucius na jami'ar Lagos Jiang Lirong ta bayyana cewa, kwalejin ya ciyar da shawarwari da hadin gwiwar al'adun kasar Sin da kasashen ketare gaba, ya kuma kara fahimtar jama'ar kasashen duniya game da Sinanci da al'adun kasar Sin, tare da ba da babbar gudumawa wajen karfafa dangantakar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, da kuma bunkasuwar al'adun kasa da kasa bisa fannoni daban daban. (Maryam)