A wajen taron manema labaran, shugabar kwalejin Confucius ta jami'ar Legas Madam Jiang Lirong ta ce, an yi gasar harshen Sinanci mai taken "Chinese Bridge" karo na farko a watan Fabrairun shekara ta 2012, abun da ya jawo hankalin bangarori da dama a Najeriya. A halin yanzu, 'yan Najeriya na nuna sha'awa sosai wajen koyon harshen Sinanci, da kokarin fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin. Makasudin shirya irin wannan gasa shi ne, a baiwa matasan Najeriya kwarin-gwiwar koyan harshen Sinanci, da ilimantar dasu game da al'adun kasar.
Madam Jiang ta kara da cewa, gasar harshen Sinanci mai taken "Chinese Bridge" ta zama wani muhimmin dandali ga al'ummar Najeriya don su kara sanin kasar Sin, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen karfafa dankon zumunci tsakanin al'ummomin kasashen biyu wato Najeriya da Sin. A halin yanzu, akwai sassan koyar da harshen Sinanci 24 a birnin Legas, kuma adadin yawan daliban da suke koyon Sinanci ya zarce dubu 3.
Bisa labarin da muka samu, an ce, za'a yi gasar harshen Sinanci karo na biyu a ranar 15 ga wata a kwalejin Confucius dake jami'ar Legas, inda daliban Najeriya za su yi takara a manyan fannoni uku, wato ilmin harshen Sinanci, rera wakokin kasar Sin, da kuma yin raye-rayen kasar Sin. Wadanda suka yi nasara, za'a basu damar kara yin karatun harshen Sinanci a kwalejin Confucius a jami'ar ta Legas. (Murtala)