An gudanar da jarrabawar Sinanci ta HSK a matakai biyu ne a jami'ar, inda dalibai 36 suka halarci jarrabawar. Bisa labarin da aka bayar, an ce, wannan ne karo na biyu da kwalejin koyon adabi ta jami'ar Lagos ta gudanar da jarrabawar HSK bayan da aka bude ta a shekarar 2012. Domin aikin koyar da Sinanci da ma'aunin koyon Sinanci na daliban kasar Nijeriya suka inganta, an gudanar da jarrabawar HSK a matakai biyu a wannan karo.
Daliban kasar Nijeriya suna begen shiga jarrabawar HSK tare da yin imani na cimma nasarar jarrabawar. Wani dalibi mai shiga jarrabawar HSK ta mataki na biyu Festus ya bayyana cewa, yana son koyon Sinanci sosai, shiga jarrabawar Sinanci zai sanya masa kaimin inganta kwazonsa na koyon Sinanci, tare da fatan cimma nasara a jarrabawar. (Zainab)