140301zabe-murtala
|
Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya INEC, ta bayyana rashin kudi, da karancin kayayyakin taimakawa shirin zabe, da ma rashin amincewa juna tsakanin masu kada kuri'u, a matsayin manyan kalubalolin da za su iya kawo cikas yayin babban zaben kasar dake tafe a 2015 mai zuwa.
Shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega ne ya sanar da haka a garin Asaba na jihar Delta, a lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar zaben jihar, tare da hadin-gwiwar hukumar INEC suka shirya. Jega ya yi alkawarin cewa, zai yi iyakacin kokarin ganin an duba wadannan batutuwa kafin lokacin zaben.
Ya ce, "har yanzu rashin isassun kayayyakin more rayuwa ne babban kalubalen da ake fuskanta a kasar, ta yadda babu hanyoyin da za'a kai ga wasu yankunan, ga rashin hasken wutar lantarki, da jiragen sama dake tashi a makare da dai sauran matsaloli."
"Duk da haka, wannan ba zai zama uzuri ba, abin da ake bukata shi ne, kyakkyawan tanadi, da hadin-gwiwa, da sanar da mutane irin matsalolin da muke fuskanta, tare da yin cikakken tanadi ga ma'aikatanmu." In ji shi.
Yayin da shugaban hukumar ke kokarin nuna muhimmancin samarwa hukumar isassun kudade, ya yi bayanin cewa duk irin shirin da za'a yi, idan har babu isassun kudi zai zama marsa amfani, ya ce da zarar an ware kudaden aikin hukumar, to kamata ya yi a sake su a kan lokaci.
Farfesa Jega ya kuma yi nuni da cewa, hukumarsa ta INEC, tana samun cikakken goyon-baya daga gwamnati, yana mai cewa kudaden albashi na ma'aikatan zaben kadai, kan lashe kaso mafi tsoka na kudaden hukumar.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.