in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karrama wasu fitattun 'yan kasa 100 a fadar gwamnatin Najeriya
2014-03-01 16:45:42 cri

A matsayin daya daga cikin muhimman bukukuwan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya, domin murnar cikar kasar shekaru 100 da dunkulewa wuri guda, a daren jiya Jumma'a an gudanar da wani kasaitaccen biki, na bada lambobin yabo ga fitattun 'yan kasa guda 100 a fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock.

Cikin mutane 100 da aka zabo, akwai rayayyu da kuma wadanda suka rasu, wadanda kuma aka yi imanin sun baiwa kasar muhimmiyar gudummawa a bangarori daban-daban cikin wadannan shekaru 100.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan biki, akwai tsaffin shuwagabannin kasar da suka hada da Cif Olusegun Obasanjo, da Janar Yakubu Gowon, da Alhaji Shehu Shagari, da Janar Muhammadu Buhari, da Janar Ibrahim Babangida, da Cif Ernest Shonekan da Janar Abdusalam Abubakar.

A bikin na jiya, bayan gabatar da jawabai da suka kunshi tarihin kasar tun daga shekarar 1914 zuwa yanzu, an kuma bayyana nasarorin da gwamnatin tarayya, karkashin shugaba Goodluck Jonathan ta cimma. Daga nan kuma aka shiga bada kyaututtuka ga mutane 100 da aka zabo. Sai dai a cewar shugaba Jonathan, wadanda suka cancanci a bawa irin wadannan kyaututtuka sun zarta 500 ba ma 100 ba, amma su ma sauran ya yi alwashin gwamnatinsa, za ta fito da wasu hanyoyi na daban domin karrama su.

An ba da kyaututtukan ne dai a manyan rukunoni guda uku, da suka hada da rukunin wadanda suka bada gudummawa a gwamnatance, da rukunin 'yan siyasa, da na shugabanni; wadanda suka bada gudummawa a fannin samarwa 'yan Najeriya ayyukan yi, da bunkasa tattalin arziki, da kuma wadanda suka sadaukar da kansu, don samowa kasar nasarori da ci gaba.

Shugaba Jonathan ya ratayawa dukkanin wadanda aka karrama lambobin girmamawa, ya kuma mika musu takardun sheda mai dauke da sunayensu, a matsayin wadanda Najeriya ta amfana da irin gwagwarmayar da suka yi domin ci gaban ta.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China