140223murtala.m4a
|
A kokarin da ta ke yi na magance ta'adin da ake samu sanadiyar barkewar gobara, gwamnatin jihar Yobe dake arewa maso gabashin tarayyar Najeirya ta samar da kudade sama da Naira Miliyan 100 don sayo kayayyakin kashe gobara na zamani da hukumar kashe gobara ta jahar za ta yi amfani da su.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin daraktan ma'aikatar kashe gobara ta jihar Yobe Alhaji Lawan Gana Bato a garin Damaturu ganin yadda ake samun yawaitar tashin gobara akai-akai a wasu sassan jihar, wanda ya zama babban kalubale ga hukumar ganin cewar, a mafi yawan lokuta saboda karancin kayayyakin aikin kashe gobarar da hukumar ke fuskanta kan haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al'ummar da bala'in gobarar ta shafa.
Daraktan ya kara da cewar, fara kama aikinsa ke da wuya a matsayin sabon darakta a wannan hukuma, ya shirya ziyara ga ma'aikatun da hukumomi gwamnatin jihar don fadakar da shugabanni kan amfanin hukumar ga al'umma.
Don haka ne yayi kira ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati gami da 'yan kasuwa da su rika kashe na'urorin wutar lantarki da suke aiki da su a shaguna su da zarar sun tashi don kaucewa barkewar gobara idan an kawo wutar lantarki da daddare lokacin da mutane ke barci a gidajensu wadda sau tari hakan kan haddasa tashin gobara.
Ya kuma roki kamfanin samar da wutar lantarki na kasa (PHCN) da ya rika samar da na'urori masu inganci na daidaita wuta da za su rika kashe kansu da zarar an samu wata 'yar matsala a lokacin da suka kawo wuta wadda hakan zai taimaka matuka wajen rage tashin gobara da ake samu lokaci zuwa lokaci a lokacin da suka kawo wuta, musamman yayin da jama'a suka rufe cibiyoyin harkokin kasuwancinsu ko kuma a ma'aikatunsu.
Daraktan ya kuma jinjina wa kokarin gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam dangane da yadda take ba da muhimmanci wajen samar da kayayyaki masu inganci ga hukumarsu don yaki da barkewar gobara, ta yadda ko da gobara ta barke, ba fata ba, hukumar kan iya tunkarar matsalar don ganin ba'a samu barna mai yawa ba.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.