in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da ajin koyon Sinanci na farko a hedkwatar kungiyar AU
2013-06-23 17:29:30 cri

Wata sanarwa daga kungiyar abokantakar kasashen Afirka da kasar Sin dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ta bayyana bude ajin koyar da yaren Sinanci irinsa na farko a hedkwatar kungiyar AU dake birnin na Addis Ababa.

Sanarwar ta bayyana cewa, an gudanar da bikin bude wannan aji, wanda cibiyar Confucius, da hadin gwiwar ofishin jakadancin kasar Sin dake Habasha suka dauki nauyin shiryawa a ranar Larabar da ta gabata.

Cikin manyan bakin da suka halarci wannan biki, akwai mataimakiyar shugaban kungiyar AU mai lura da harkokin gudanarwa da mulki Rekia Mahamoudou, da ma'aikatan kungiyar ta AU, da kuma jami'an ofishin jakadancin kasar Sin. Da take jawabi yayin taron Rekia ta yabawa ofishin jakadancin kasar Sin bisa wannan yunkuri nasa, wanda tace zai taimaka matuka wajen musayar al'adu tsakanin kasar Sin da sauran sassan nahiyar Afirka. Yayin bikin na ranar Laraba an nuna wani fim dake kunshe da tarihin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China