in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar jiragen kasa na birnin Makka da Sin ta gina ta taimaka yadda ya kamata
2011-11-10 14:30:16 cri

Ranar Laraba 9 ga wata, hanyar jiragen kasa na birnin Makka da kamfanin gina hanyar jiragen kasa na kasar Sin ya gina ta taimakawa mahajjata yadda ya kamata a wannan shekara. A tsawon kwanaki 7 da aka shafe ana jigilar mahajjata daga ran 3 ga wata, an yi jigila sau 1700, yawan mahajjatan kasa da kasa da aka yi gijilar ya kai miliyan 3.2.

Bisa labarin da jaridar Asharq Alawsat ta kasar Saudiyya ta bayar, an ce, an yi amfani da wannan hanyar jiragen kasa yadda ya kamata. Mahajjatan da aka yi jigilar sun hada da masarautar kasashen Larabawa, ministocin kasa da kasa da dai sauransu. Dukkansu sun jinjinawa aikin da kamfanin gina hanyar jiragen kasa na kasar Sin ya yi.

An ba da labari cewa, dukkan mahajjatan sun tafi wurare uku na aikin hajji na birnin Makka wato Mina, Muzdalifah da Arafat ta hanyar jiragen kasa. Wannan ya taimaka wajen magance matsalar cunkoson hanyoyi a lokacin aikin hajji har ma ya taimakawa mahajjatan wajen gudanar da aikin hajji cikin sauki.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China