in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahajjatan kasashen duniya sun fara aikin hajji na bana
2012-10-24 20:39:06 cri

Ya zuwa ranar 24 ga wata, mahajjata kusan miliyan 3 wadanda suka fito daga yankuna daban daban na duniya bi da bi sun isa zirin Mina dake wajen birnin Mecca na kasar Saudiyya, inda suka fara aikin hajjin bana da za a shafe kwanaki biyar ana yinsa.

Hukumomin tsaro, kwana-kwana, kiwon lafiya, kula da harkokin ruwan sha da wutar lantarki, zirga-zirga na kasar Saudiyya sun kuntsa matuka domin tabbatar da ganin an tafiyar da harkokin aikin hajji lami lafiya.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, musulmai kimanin dubu 13.8 na kasar Sin sun je Mecca domin wannan aikin hajji a bana. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China