Tawagar Alhazai na kasar Sin dai an saukar da su ne a dab da Harami a birnin Makkah. Tun daga ran 6 ga wata zuwa ran 28 ga watan na Oktoba, yawan maniyata da suka isa Saudiyya daga larduna da birane 28 da suka je sauke farali a Saudiyya ya kai dubu 13.781, kuma a ran 3 ga wata da dare, suka bi sahun sauran Alhazai zuwa Mina.
Aikin hajji na daya daga cikin muhimman ayyuka 5 da addnin musulunci ya kayyade, kuma ya kamata ko wane musulmi da ya samu hali ya yi aikin hajji a birnin Makka.