An fara gina wannan hanyar dogo daga shekarar 2008. A ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar bana, za a fara aiki da hanyar gaba daya, kuma ana sa ran zai yi jigilar fasinjoji kusan miliyan uku cikin tsawon kwanaki biyar. A lokacin aikin hajjin bana, musulman da a baya su kan shiga motoci zuwa wuraren aikin hajji za su shiga kananan jiragen kasa, abin da zai rage cunkuson motoci da a kan yi fama da shi a lokacin aikin hajji. (Lubabatu)