A labarin da kamfnain dillancin labarai na MENA na kasar Masar ya bayar, an ce, bayan da kasar Saudiyya ta sanar da rufe ofishin jakadancinta a kasar Masar tare da dawo da jakadanta a wannan rana, Mohamed Hussein Tantawi, shugaban kwamitin kolin rundunar sojin kasar Masar ya aika da sako ga sarkin kasar Saudiyya, Abdullah Bin Abdul-Aziz, inda ya yi fatan ganin Saudiyya za ta iya sake yin tunani a game da wannan kuduri, kuma ya sake jaddada irin huldar 'yan uwantaka da ke tsakanin kasar Masar da ta Saudiyya.
Daga ranar 24 zuwa 27 ga wannan wata, daruruwan 'yan kasar Masar sun yi ta yin zanga-zanga a ofishin jakadancin kasar Saudiyya da ke kasar ta Masar, inda suka yi kira ga Saudiyya da ta sako wani lauyan kasar Masar da ta kama. A ranar 28 ga wata, gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa, sakamakon yadda ofishin jakadancinta da ke Masar ke fuskantar barazana daga masu zanga-zangar, ta yanke shawarar rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Alkahira da kuma kananan ofisoshin jakadancinta da ke biranen Suez da kuma Alexandria, tare da dawo da jakadanta.(Lubabatu)