in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Layin dogo na Makkah da ke Saudiya ya fara aiki a lokacin aikin hajjin bana a hukunce
2012-10-26 16:22:51 cri
Tun daga karfe 12 na safiyar ranar 23 ga watan Oktoban shekarar da muke ciki, bisa agogon wurin, layin dogo da ke cikin birnin Makkah na kasar Saudiya da kamfanin gina layukan dogo na kasar Sin ya gina ya fara aikin jigilar maniyyata aikin hajji na shekarar 2012 a hukunce, ya zuwa karfe 12 na daren ranar 29 ga wannan wata, zai gama aikinsa na bana, a halin yanzu, yana aiki yadda ya kamata.

A halin da ake ciki yanzu, layin dogo na Makka ya kasance layin dogon da ke birnin da aka gina da fasahar zamani cikin gajeren lokaci, wanda kuma makin digirin dake wajen taragun jiragen kasa ya fi zafi a duniya. A yayin aikin hajji na bara, gaba daya jiragen kasa sun yi jigila ta wannan layin dogo har sau 1765, kuma maniyyata aikin hajjin da aka yi jigilar su sun kai wajen miliyan 3.224.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China