in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da sayarwa Saudiyya makamai da kudinsu ya doshi dala biliyan 30
2011-12-30 16:52:24 cri

Ranar Alhamis 29 ga wata, fadar shugaban kasar Amurka ta sanar da cewa, Amurka za ta sayarwa Saudiyya makamai da yawan kudinsu ya kai kusan dala biliyan 30.

Kakakin fadar Josh Earnest ya ba da sanarwa cewa, Amurka da Saudiyya sun sa hannu kan wata yarjejeniyar sayarwa kasar Saudiyya makamai da yawansu ya kai dala biliyan 29.4. Bisa wannan yarjejeniyar, Amurka za ta sayarwa kasar Saudiyya jiragen saman yaki mai lamba F-15SA guda 84 tare da taimakawa kasar wajen kyautata yanayin jiragen saman yaki masu lamba F-15S guda 70 da Saudiyya take da su.

An ba da labari cewa, a watan Oktoba na bara, Amurka ta sanar da cewa, za ta sayarwa kasar Saudiyya makamai da yawan kudinsu ya kai dala biliyan 60 cikin shekaru 15 zuwa 20 masu zuwa. Jami'in gwamnatin Amurka ya bayyana shirin sayarwa kasar Saudiyya makamai da zummar taimakawa kanta wajen tabbatar da burinta a fannin diplomasiyya tare da tabbatar da moriyar Amurka a yankin gabas ta tsakiya.

Kafofin yada labaru na kasar Amurka suna ganin cewa, gwamnatin Amurka na nuna damuwa ga karuwar karfin Iran a yankin Gulf bayan Amurka ta janye sojojinta daga Iraqi. Bisa halin da ake ciki, gwamnatin Amurka na neman kara karfin kasashe kawayenta dake Gulf domin hana karuwar karfin Iran a yankin.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China