in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahajjata Sinawa sun isa Sauddiya
2012-10-15 16:33:26 cri

Ranar 14 ga wata, jagoran mahajjata Sinawa kuma mataimakin shugaban kungiyar kula da harkokin addinin Musulmi ta kasar Sin Hong Changyou ya bayyana cewa, musulmai Sinawa kimanin dubu 13.8 dukkansu sun isa birnin Makka na kasar Saudiyya, kuma za su fara aikin hajji daga ran 24 ga wata.

Hong Changyou ya bayyana cewa, wadanda suka gana da shi bayan isarsa, ciki har da jakadan kasar Sin dake Saudiyya Li Chengwen, karamin jakadan Sin dake birnin Jeddda Wang Yong, sanna za a raba mahajjata Sinawa zuwa rukunoni tara, kuma za a saukar da su a Otel-otel 9 dake kewayen babban masallacin Makka.

Bisa labarin da aka bayar an ce, Sin ta samar musu masu aikin jiyya da masu kula da harkokin addini gare su domin tabbatar da lafiyarsu ta yadda za su kammala aikinsu yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China