Ofishin taimakawa matalauta da kawar da talauci na kasar Sin ya bayyana a yau din nan Litinin 27 ga wata cewa, ko da yake, Sin ta kai matsayin biyu ta fuskar tattalin arziki, amma yawan Sinawa da suke fama da talauci ya kai miliyan 100, hakan ya sa, Sin na bukatar taimako daga kasa da kasa sosai, saboda haka, Sin na maraba da taimako daga kasa da kasa.
A gun wani taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya yi, ofishin ya ce, yin hadin kai da kasa da kasa wajen kawar da talauci wata muhimmiyar fasaha ce da Sin ke mallaka, ci gaban da Sin take samu wajen kawar da talauci ya kunshe da taimakon da kasa da kasa suka bayar.
Ban da haka, Sin kuma na bukatar nazarin wasu batutuwa masu musamman dangane da talauci, da kuma yin ayyukan gwaji, da kara mu'ammala da kasa da kasa kan fasahar kawar talauci, da sa kaimi ga wannan aiki yadda ya kamata. (Amina)