Zaman taron na yini guda ya taimakawa mahalarta taron kimanin 120 da suka hada da kusoshin 'yan siyasa, masana, shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da kuma masu zuba jari ya taimaka masu fahimtar manufofin yaki da talauci da kasar Sin ta aiwatar a tsawon karni uku.
A yayin da yake jawabi gaban mahalarta taron, shugaban kasar Tanzania Jakaya Kikwete ya nuna cewa wannan haduwa ta zo bayan dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afrika karo na 5 da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, kuma wata dama ce mai kyau, wadda ta kasance hanya guda ta aiwatar da matakan da aka cimma a Beijing.
Kimanin kashi 70 cikin 100 na mutanen Afrika dake yankin Sahel na zaman rayuwa a yankunan karkara kuma suna dogaro da noma, a yayin da kuma Afrika take amfani da kayayyaki kalilan na zamani a wannan fanni, da har yanzu yake a matsayi na kasa, in ji shugaba Kikwete. Hakazalika ya bayyana matsalar karancin abinci da kasashen Afrika da yawa suke fuskanta.
A nasa jawabin, jakadan kasar Sin dake kasar Tanzania, Lu Youqing ya bayyana cewa wannan taro na 3 kan kawar da talauci na shaida niyyar da kasar Sin ta dauka zuwa kasashen Afrika kuma ta kasance wani sabon yunkuri na shawarwari da dangantaka tsakanin Sin da Afrika.
Wannan dandali da cibiyar kasa da kasa domin kawar da talauci ta kasar Sin (IPRCC) ta dauki nauyin shiryawa tare da hadin gwiwar tsarin ci gaba na majalisar dinkin duniya PNUD, ya kasance wani muhimmin dandalin yin musanya kan harkokin bunkasuwa tsakanin Sin da Afrika. (Maman Ada)