Kwanan baya an gudanar da bikin baiwa 'yan tattalin arziki lambar yabo a fannin hadin gwiwar tsakanin Sin da Afrika na shekarar 2012, tare da gabatarwa nahiyar Afrika kamfanonin kasar Sin 100 mafiya nagarta karo na biyu a nan birnin Beijng.
Wannan dai taro na da zummar kawo babban tasiri ga matakan da Sin ke dauka dangane da nahiyar Afrika, da goyon bayan taron koli karo na biyar na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika, da kuma yabawa 'yan masana'antu, da sauran mutane da suka ba da taimako matuka wajen yin hadin kai tsakanin bangarorin biyu ta fuskar cinikayya.
Mukadashin jakadan kasar Masar mai kula da harkokin ciniki dake kasar Sin dokta Ayman Aly Osman, ya yabawa taimakon da dandalin hadin kai da raya masana'antun kasashen Sin da Afrika ya bayar wajen habaka hadin kai tsakanin bangarorin biyu, wanda kuma ya karfafa gwiwar 'yan kasuwan kasar Sin wajen zuba jari a kasashen waje, tare da sa kaimi ga ciniki da zuba jari tsakanin bangarorin biyu.
An ce, wannan taro ya ba da damar mika wadannan lambobin yabo iri 2, bisa ma'aunin bai daya wato yawan moriyar da aka samar wajen bunkasuwar zaman al'ummar nahiyar Afrika. (Amina)