Bisa labarin da aka samu, an ce, daliban da za a dauka cikin wannan shiri za su shafi gundumomi masu fama da talauci 680 da ke lardunan 21 a kasar, haka kuma jami'o'in da za su aiwatar da wannan shiri, za su dauki dalibai a fannonin aikin gona da albarkatun ruwa da nazarin albarkatun kasa da ilmin likitanci da dai makamantansu, bisa bukatun raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a yankunan da ke fama da talauci na kasar.
Haka kuma, bayan da daliban suka kammala karatu, za su koma garinsu domin ba da hidima a yankuna mafi fama da talauci, kuma za su samu manufofi masu gatanci kamar samun kudin bonas ko rance wajen biyan kudin karatu.(Bako)