Rahoton ya yi bincike kan mutane masu fama da talauci a nahiyar Afirka tun daga shekara ta 2005 zuwa ta 2008, kuma ya nuna cewa, ko da yake yawan mutane a nahiyar yana karuwa a lokacin, amma yawan mutane masu fama da talauci ya ragu daga miliyan 395 a shekarar 2005 zuwa miliyan 386 a shekarar 2008.
Hakazalika kuma rahoton ya nuna cewa, duk da haka kuwa, har ila yau yankin kudu da Sahara tana kasancewa yanki mafi talauci a duniya.(Zainab)