Don haka, ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara mai da hankali tare da zuba jari kan makomar daukacin bil Adama, masamman ma a fuskar ba da taimako ga masu fama da talauci.
Babban taken ranar kawar da talaucin bana shi ne: kawo karshen tashe-tashen hankula da talauci ya haifar da kuma inganta zaman lafiya a duk fadin duniya.
A cikin jawabin nasa, Ban Ki-moon ya nuna cewar, ba tausayi ne kawai masu fama da yunwa da talauci da kuma rashin mutuntawa suke bukata ba, babbar bukatarsu ita ce samun hakikanin kyakyawan taimako mai inganci.
Ban Ki-moon ya kara da cewa, kasashe da yawa suna fuskantar raguwar tattalin arziki, saboda gwamnatocin kasashen suke kokarin daidaita kasafin kudi domin samun kawar da barazanar karancin kudi kan aikin kawar da talauci. Ya jaddada cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan ba da hidimar jama'a, tabbacin kudin shiga, samar da ayyuka nagari da kuma tsaron zamantakewar al'umma ga masu fama da talauci, ta yadda za a iya cimma burin kafa zamantakewar al'umma mai karfi da wadata, bai kamata ba a lahanta moriyar matalauta.(Maryam)