A lokacin taron na kwanaki uku, manyan jami'an gwamnati fiye da hamsin da masana da kuma 'yan kasuwa daga Sin da kasashen Africa har ma da wakilan kungiyoyi na duniya za su tattauna yadda za'a rage radadin talauci.
''Sin tana da niyyar nuna dabarun da ta yi amfani da su tare da sauran kasashen duniya musamman kasashen nahiyar Africa don karfafa hadin kai tsakanin kasa da kasa ta wannan fanni da sauran fannoni na cigaba'',in ji Zheng Wenkai, mataimakin darekta a cibiyar dake kula da sha'anin ayyukan yaye talauci da kuma samun cigaba.
Cibiyar bullo da dabarun yaye talauci ta Duniya dake nan kasar Sin ita ta shirya wannan taron tare da hadin gwiwar ofishin dake MDD da kuma Jami'ar Shenzhen.(Fatimah)