Shugabar hukumar raya kasa ta MDD Helen Clark ta furta a ran 17 ga wata a nan birnin Beijing cewa, duk da cewar ana fama da kalubale sosai a fannin tattalin arzikin duniya, amma ana sa ran za a cimma burin rage rabin yawan matalauta da MDD ta tsara kafin shekarar 2015.
Ranar 17 ga watan Oktoba rana ce ta yaki da kangin talauci ta duniya. Helen Clark ta halarci taron a wannan rana a birnin Beijing, kuma ta bayyana a yayin da take ganawa da manema labaru cewa, kasar Sin ta yi iyakacin kokari wajen cimma burin shirin rage yawan matalauta na MDD. Tun daga shekarar 1981 zuwa shekarar 2005, kasar Sin ta cimma nasarar fitar da mutane miliyan 550 daga kangin talauci.
Helen Clark ta ce, sabo da sakamako mai kayu da kasar Sin ta samu wajen rage yawan matalauta, ganin cewa kasar na da mutane masu dimbin yawa, shi ya sa, kasar Sin ta ba da babbar gundummawa wajen cimma burin rage rabin yawan matalauta na MDD daga shekarar 1990 zuwa shekarar 2015. Hukumar raya kasa ta MDD tana dukufa kan yada sakamako mai kyau da kasar Sin ta samu zuwa dukkan fadin duniya. (Lami)