in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da masana'antu masu zaman kansu suka samu ya haura kashi 60 bisa dari na GDP a kasar Sin
2013-02-04 17:19:50 cri
Bisa labarin da aka samu daga jaridar tattalin arziki ta rana-rana, an ce, cikin farkon watanni 11 na shekarar 2012, jarin da masana'antu masu zaman kansu suka zuba domin samun kadarori a birane da garuruwa ya kai yuan biliyan 19900, adadin ya karu da kashi 25.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2011, ya kuma kai kashi 61.1 bisa dari na dukkan jarin da aka zuba a wannan fanni.

Hakan ya sa, a shekarar 2012, yawan kudin da masana'antu masu zaman kansu suka samu ya haura kashi 60 bisa dari na GDP na kasar Sin.

Bisa labarin da aka samu, ya zuwa watan Satumba na shekarar 2012, yawan kamfanoni masu zaman kansu da aka yi rajista a kasar Sin ya haura miliyan 10, dake kunshe da ma'aikata fiye da miliyan 110, wadannan kamfanoni kuma suna da babban karfi wajen samar da guraben aikin yi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China