in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nazarci yanayin tattalin arziki da ake ciki yanzu
2013-04-25 20:50:55 cri
A ranar Alhamis 25 ga wata, zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi taro, inda aka nazarci yanayin tattalin arziki da ake ciki, da harkokin tattalin arzikin kasar. Mr. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar shi ne ya shugabanci taron, kuma ya yi wani muhimmin jawabi.

A yayin taron, an ce, dole ne a yi kokarin kara bukatun da ba za su gurbata muhalli ba a kasuwannin cikin gida. Kana dole ne a kara bunkasa tattalin arzikin dake da nasaba da kasuwannin kasashen duniya, kara bude kofofin ayyukan ba da hidima ga kasashen waje, nuna goyon baya ga kokarin zuba jari a kasashen waje kan muhimman fannoni da ayyuka. Sannan dole ne a yi kokarin tabbatar da farashin kayayyaki da kyautata tsarin masana'antu, ta yadda za a iya kara bunkasa sabbin masana'antu masu muhimmanci. Kuma ya kamata a hanzarta neman dabarun magance gurbata muhalli da koguna da ruwan dake karkashin kasa. Bugu da kari, ya kamata a dauki matakan mayar da yankuna masu karkara da su zama garuruwa domin neman ci gaba cikin daidaito tsakanin yankuna daban daban.

Haka kuma, a yayin taron, an jaddada cewa, za a kara yin kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a da aikin ceto a yankin da bala'in girgizar kasa na Lushan ya shafa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China