in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alkaluman sayar da kayayyakin masana'antun kasar Sin ya sauka a watan Afrilu
2013-05-01 16:41:02 cri

Hukumar kula da harkokin saye da sayar da kayayyakin kasar Sin(CFLP) ta fada a Yau Laraba 1 ga watan Mayu cewa, alkaluman sayar da kayayyakin masana'antun kasar Sin PMI sun fadi zuwa kashi 50.6 cikin 100 a watan Afrilu daga kashi 50.9 cikin 100 a watan Maris.

A cewar sanarwar da hukumar ta CFLP ta bayar, wannan ya kasance watanni bakwai ke nan a jere da alkaluman na PMI ke kasancewa sama da kashi 50 cikin 100, matakin da ke bambanta karuwar ci gaba daga raguwar harkokin sayar da kayayyaki.

Sanarwar ta ce, ko da ya ke alkaluman ba su canja ba, amma dan karamin canjin yana nuna raguwar ci gaban bangaren masana'antu kuma akwai bukatar a kara himma wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin.

Wani mai sharhi dake cibiyar binciken ci gaba a majalisar gudanarwar Sin Zhang Liqun, ya ce alkaluman PMI na watan Afrilu ya nuna cewa, asusun farfado da tattalin arzikin Sin ba shi da karfi sosai. Don haka ya ce kamata ya yi a kara kokari wajen daidaita bukatun cikin gaba, matakin da ya ce zai taimaka wajen warware koma bayan alkaluman na PMI. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China